EPISODE · May 27, 2026 · 14 MIN
Kanun Labaran Hausa na Babbar Salla 2026-05-27 (HausaRadio.net Headlines)
from Hausa Newsletter · host Hausa Radio News Headlines
Ƙarin bayani: https://hausadictionary.com/HausaRadio.net/2026-05-27== BBCHausa Safe 2026-05-27 ==Mai gabatarwa: Aisha Sharif Baffa#1 🎧 @0:17 Lebanon ta ce an kashe mutane talatin da ɗaya a hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a jiya Talata.#2 🎧 @0:26 Ghana ta fara mayar da ɗaruruwan ƴan ƙasarta gida daga Afirka ta Kudu bayan zanga-zangar ƙyamar baƙin haure.#3 🎧 @0:31 A Najeriya, yayin da ake ci gaba da dakon sakamakon zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, jam’iyyar ta yi ƙarin haske kan abin da ya janyo jinkiri wajen sanar da sakamakon.#4 🎧 @1:03 BBC Hausa ta ce za a ji ƙarin bayani kan abubuwan da ya kamata mai zuwa Sallar Idi ya yi, da kuma wanda zai yi layya.== BBCHausa Hantsi 2026-05-27 ==Mai gabatarwa: Aisha Sharif Baffa#5 🎧 @1:27 Ma’aikatan kamfanin lantarki na Samsung sun dakatar da yajin aikin da suka shiga bayan cimma matsaya kan biyan su kuɗaɗen alawus.#6 🎧 @1:41 A Najeriya, bayan tsohon ministan sadarwa Farfesa Ali Isa Pantami ya rasa damar zama ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Gombe, ya sauya sheƙa zuwa PDP inda aka ba shi takarar.#7 🎧 @2:11 A Najeriya, manoma da dama na barazanar ƙin noma kayan abinci kamar masara da gero, suna cewa za su fi mayar da hankali kan noman kayan sayarwa kamar waken soya da gyada.== BBCHausa Rana 2026-05-27 ==Mai gabatarwa: Aisha Aliyu Jafar#8 🎧 @3:22 Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo na cikin hali na tsaka mai wuya, inda take fama da ɓarkewar cutar Ebola da kuma rikici.#9 🎧 @3:37 Ghana ta kwashe rukunin farko na ƴan ƙasarta daga Afirka ta Kudu sakamakon zanga-zangar ƙyamar baƙin haure.#10 🎧 @3:47 A Najeriya, Majalisar Ba da Shawara kan Harkokin Jam’iyyun Siyasa ta buƙaci Shugaba Tinubu ya ƙara himma wajen yaƙi da ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga a faɗin ƙasar.#11 🎧 @4:12 Al’ummar Musulmi na ci gaba da gudanar da shagulgulan bikin Babbar Sallah a faɗin duniya, duk da ƙorafe-ƙorafe kan tsadar rayuwa da ta hana wasu yin layya.== BBCHausa Yamma 2026-05-27 ==Mai gabatarwa: Aisha Aliyu Jafar#12 🎧 @5:23 Rundunar sojin Isra’ila ta bai wa al’ummar da ke zaune a baki ɗayan kudancin Lebanon umarnin ficewa.#13 🎧 @5:34 Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi kira da a tsagaita wuta a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo domin samun damar dakile yaɗuwar Ebola.#14 🎧 @5:43 A Najeriya, masana tsaro sun fara tsokaci kan rahoton Amurka da ke cewa a ƴan shekarun nan wasu masu gwagwarmaya da makamai daga tsatson Fulani na kai miyagun hare-hare kan al’ummomi.#15 🎧 @6:14 A Najeriya, ranar 27 ga watan Mayu ta kasance Ranar Yara, inda ake tambayar halin da yaran ƙasar ke ciki a ɓangarorin ilimi, lafiya, zamantakewa da tsaro.== DWHausa Safe 2026-05-27 ==Mai gabatarwa: Muhammad Awal Balarabe#16 🎧 @7:19 Musulmai a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na hawan Sallah cikin halin ɗar-ɗar sakamakon barazanar hari da hukumomi suka ja hankali a kai.#17 🎧 @7:37 DW Hausa ta ce za a ji abubuwan da Musulmi ya kamata ya yi a ranar Idi.#18 🎧 @7:41 Gwamnatin Ghana ta buɗe ƙofofinta ga ɗaukacin ƴan nahiyar Afirka ta hanyar ba da visa kyauta.#19 🎧 @7:49 A Sudan, tsadar man fetur na barazanar jefa ƙasar cikin matsananciyar ƙarancin abinci.#20 🎧 @7:54 Za a ji inda aka kwana game da shirin Shugaba Trump na gindaya wa baƙi tsauraran sharuɗɗa kafin ba su katin zama ɗan ƙasa.#21 🎧 @8:13 Al’ummar Gaza na gudanar da Idin Babbar Sallah cikin mawuyacin hali sakamakon lalacewar gine-gine da tsadar rayuwa.#22 🎧 @8:20 Iran ta zargi Amurka da karya matakin tsagaita wuta da ke tsakaninsu bayan hare-haren da aka kai mata ta sama.#23 🎧 @8:24 Koriya ta Arewa ta yi gwajin sabbin makamai masu linzami masu amfani da fasahohi iri daban-daban.== DWHausa Rana 2026-05-27 ==Mai gabatarwa: Musa Tijjani Ahmad#24 🎧 @8:54 Al’ummar Musulmi a faɗin duniya na gudanar da bikin Sallar Idi a yanayi daban-daban.#25 🎧 @9:04 Shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, Janar Abdurrahman Tchiani, ya yi Sallar Idi a birnin Yamai.#26 🎧 @9:08 Al’ummar jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya sun gudanar da Sallar Idi cikin yanayin cikakken tsaro sakamakon barazanar kai hare-haren ta’addanci.#27 🎧 @9:17 Amurka ta sake jaddada zargin cewa wasu makiyayan Fulani sama da dubu talatin na da hannu a tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Najeriya, yayin da shugabannin makiyaya ke mayar da martani.#28 🎧 @10:18 Isra’ila ta yi iƙirarin kashe shugaban wani ɓangare na ƙungiyar Hamas a zirin Gaza.#29 🎧 @10:23 Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya buƙaci a wanke shi daga zargin hannu a badakalar zaɓen Libya.#30 🎧 @10:30 An ceto mutanen da ambaliya ta rufe a kugu tsawon mako guda a Thailand.== DWHausa Yamma 2026-05-27 ==Mai gabatarwa: Musa Tijjani Ahmad#31 🎧 @10:58 An gudanar da Sallar Idi cikin yanayi na fargabar tashe-tashen hankula a wasu yankunan Gabas ta Tsakiya.#32 🎧 @11:05 A jihar Kano ta Najeriya, babban abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne bai wa sarakuna biyu cikakken ikon gudanar da Sallar Idi.#33 🎧 @11:32 Gwamnatin jihar Legas ta bijiro da tsarin kare haƙƙin masu zama a gidaje da shagunan haya a birnin domin kare su daga barazanar masu dukiya.#34 🎧 @11:41 Ƙasar Senegal ta shiga wani yanayi na tsaka mai wuya bayan takun-saka tsakanin Shugaba Bassirou Diomaye Faye da tsohon Firayim Minista Ousmane Sonko.#35 🎧 @12:16 Dakarun Isra’ila sun kashe sama da mutane talatin a wani farmaki kan wasu yankunan ƙasar Lebanon.#36 🎧 @12:22 Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da wani rahoton yarjejeniyar zaman lafiya da Iran.#37 🎧 @12:27 Ƴan ƙasar Ghana ɗari uku sun koma gida daga Afirka ta Kudu bayan hare-haren ƙyamar baƙi.== RFIHausa Yamma 2026-05-27 ==Mai gabatarwa: Hawa Halliru Gwangwazo#38 🎧 @12:36 Amurka ta gano yadda wasu ƴan ta’adda fiye da dubu talatin ke ƙaddamar da hare-hare a sassan Najeriya.#39 🎧 @12:45 Ƙungiyar Human Rights Watch ta zargi Daular Larabawa da ɗaukar hayar sojojin Colombia domin taimaka wa RSF a yaƙin Sudan.#40 🎧 @12:50 Mahajjata sun gudanar da ibadar jifan shaiɗan cikin yanayi na tsananin zafi, yayin da al’ummar Musulmi ke bukukuwan Babbar Sallah a faɗin duniya.== CRI / CGTN Hausa 2026-05-27 ==#41 🎧 @13:39 Yawan ribar da manyan masana’antun sarrafa hajoji na ƙasar Sin suka samu a watanni huɗu na farkon shekarar bana ya ƙaru da kaso sha takwas da ɗigo biyu bisa ɗari.#42 🎧 @13:44 An ƙaddamar da bikin gabatar da fina-finan ƙasar Sin a ƙasashen waje a Johannesburg.#43 🎧 @13:55 Tarayyar Afirka ta yi kira da a sake ƙoƙarin raya nahiyar Afirka. This is a public episode. If you would like to discuss this with other subscribers or get access to bonus episodes, visit hausa.substack.com
NOW PLAYING
Kanun Labaran Hausa na Babbar Salla 2026-05-27 (HausaRadio.net Headlines)
No transcript for this episode yet
Similar Episodes
Aug 19, 2025 ·1m
Aug 12, 2025 ·40m
Jul 1, 2025 ·28m
Jun 24, 2025 ·38m