EPISODE · Mar 22, 2026 · 3 MIN
Kanun Labaran Hausa na Lahadin 2026-03-21
from Hausa Newsletter · host Hausa Radio News Headlines
2026-03-22 Sunday-LahadiBBC Hausa SafePartial YT | Mai gabatarwa: Muhammad Annur Muhammad* Makamai masu linzami na Iran sun faɗa kan wasu garuruwa biyu na kudancin Israel da suka raunata sama da mutum ɗari ɗaya (100+), inda ɗaya ya faɗa kusa da wata muhimmiyar cibiyar nukiliya ta Israel.* Shugaba Trump ya yi barazanar tarwatsa gaba ɗayan tashoshin samar da lantarki na Iran idan har gwamnatin ƙasar ta ƙi ta buɗe mashigar Hormuz cikin sa’a arba’in da takwas (48 hours).* Gwamnatin Najeriya ta ɓullo da wani tsari na koyar da ɗaliban makarantun tsangaya harshen Larabci maimakon karatun Alƙur’ani zalla. Ko me ya sa?* In ka kawo masa fassarar da ba dai dai ba ce, don kana so ka ko ya shiga ƙungiyarka, ka ya shiga wani abun da zai cuci ƙasar nan, zai ce ‘Allah Ya gafarta Malam, wannan fassarar ta ka ba ta yi dai dai da harshen Larabci ba saboda ni ma yanzu ina ji.’* Har wa yau a Najeriyar, bayanai na ƙara fitowa fili kan yadda wasu ‘yan bindiga suka sace sakataren ƙaramar hukumar Kibiya a jihar Kano (Hamza Durya).* Yaronsa da yake kwana a ɗakin waje, su ka buga mai ƙofa ya fito, inda kai tsaye suka sa masa wuƙa a wurin. Su ka ce ya je ya gaya wa mahaifinsa cewa cikinsa yana ciwo. Suka samu damar buɗewa yana buɗewa, suka danna suka shiga.* Akwai Karatun Labarin Gasar Hikayata na BBCDW HausaCikakken shirin | Mai gabatarwa: DW Hausa’s Fauziyya Dauda* Ana samun ƙaruwar mata a harkar siyasa yayin da ƙasashe da dama a Afirka za su gudanar da zaɓe na ƴan majalisar dokoki zuwa nan da ƙarshen shekarar 2026.* A Amurka kuwa za a ji yadda wasu jihohi suka fara gudanar da zaɓen fitar da gwani (primaries) da za su wakilci jam’iyyunsu gabanin zaɓen rabon wa’adi (midterms).* Yayin da ake bikin ranar ruwa ta duniya (World Water Day 2026) a yau, za mu je jihar Kano a tarayyar Nijeriya domin jin yadda matsalar rashin ruwa ta zame masu ƙarfin ƙafa da ma dalilan da suka sanya ake wahalar sa har yanzu a jihar.* Muna tafe da sharhunan jaridun Jamus akan nahiyar Afirka da ma rahoton nan na musamman na kundin ƴan mata.* Gwamman mutane sun jikkata a hare-haren da Iran ta kai kudancin Isra’ila.* Shugaba Trump na Amurka ya yi barazanan lalata dukkannin cibiyoyin lantarkin Iran.* ‘Yan sanda sun kama masu fafutuka da dama a Zimbabwe.RFI HausaCikakken shirin | STT | Mai gabatarwa: Michael Kuduson* Amurka ta ɗage takunkumi na wucin gadi akan ɗanyan man Iran da aka riga aka loda wa jiragen ruwa kuma su ke kan teku.* Rundunar sojin Najeriya ta ce ta halaka ɗinbi ‘yan ta’adda a jihar Borno tare da daƙile hare-haran jirage marasa matuƙa (Unmanned Aerial Vehicles, UAVs).* Cocin Pentikostal (Pentecostal churches) Rwanda ta sauke wasu fastoci talatin da biyar (35 pastors) daga muƙamansu sakamakon rawar da suka taka a kisan kiyashi da aka yi wa ƴan ƙabilar Tutsi shekaru kusan talatin da biyu da suka wuce (about 32 years ago). This is a public episode. If you would like to discuss this with other subscribers or get access to bonus episodes, visit hausa.substack.com
NOW PLAYING
Kanun Labaran Hausa na Lahadin 2026-03-21
No transcript for this episode yet
Similar Episodes
Aug 19, 2025 ·1m
Aug 12, 2025 ·40m
Jul 1, 2025 ·28m
Jun 24, 2025 ·38m