Skip to content
Al'adun Gargajiya podcast artwork

Al'adun Gargajiya

by RFI Hausa

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

From the show's RSS feed, refreshed Oct 27, 2026. Source feed.

Subscribe Bookmark

Episodes

  1. Mahukunta na yunkurun sake rubuta tarihin Jamhuriyyar Nijar

    Shirin Al'adun Mu Na Gado na wannan mako yayi duba ne kan yunƙurin sake rubuta tarihin Jamhuriyyar Niger da magabatan ƙasar suka dauri aniyar yi. Tun bayan juyyin milki da sojojin ƙasar Niger suka yi da niyar raba gari da suka yi da duk wani gadon Turawan mulkin mallaka da suka mullaki ƙasar, sun...

  2. Yadda al'ummar Hausawa kusan dubu 30 ke rayuwa a tsakanin ƙabilun ƙasar Togo

    Shirin al’adun mu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan karon ya leka ƙasar Togo ne, inda muka yi ƙoƙarin jin yadda Hauasawan wannan ƙasa ke rayuwa. A Togo dai akwai kimanin Hasauwa dubu 30 da ke rayuwa da sauren ƙabilun wannan ƙasa ba tareda wata matsala, dai dai gwalgwado dangantaka na tafiya...

  3. Bikin al'adun makiyaya na ƙasa a Jamhuriyar Nijar

    'Al’adunmu Na Gado' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya sake yin tattaki ne zuwa garin Ingal da ke Yankin Agadez a Jamhuriyyar Nijar, inda aka gudanar da bikin ala’adu na ƙasa baki ɗaya da ke haɗa makiyaya daga ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee'. An dai saba gudanar da...

  4. Mahukuntan Nijar sun karrama fitaccen mawaƙin gargajiya Mamman Gawo Filinge

    Da yake mawaƙan gargajiya na da matuƙar tasiri a ƙasar Hausa, mahukunta sun karrama fitaccen mawaƙin Nijar, Marigayi Alhaji Mamman Gawo Filinge, inda aka raɗawa wani titi sunansa. Mawaƙin ya taka gagarumar rawa sakamakon waƙokinsa na siyasa da na gargajiya, da noma da kuma zamantakewa, lokacin da...

  5. Jamhuriyar Nijar ta gudanar da bikin ranar Hausa ta bana a ƙasar

    Shirin Al’adumu na gado a wannan makon ya sake waiwayar baukukuwan ranar Hausa ne ta Duniya, ranar da babban taronta ke gudana a dukkanin ranakun 26 ga watan Agusta duk shekara, to amma kasancewar bikin ya samu karɓuwa a gwamman ƙasashe ya sa bayan babban taron ake gudanar da wasu ƙarin bukukuwan...

  6. Muhawara kan banbance tsakanin ƙabilun Hausawa da kuma Fulani a Najeriya

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon ya mayar da hankali kan zamantakewa da auratayyar ƙabilun Hausawa da Fulani, ƙabilu 2 da suka juye zuwa Hausa Fulani bayan zaman tare na tsawon shekaru musamman a Najeriya. A baya-bayan nan muhawara ta fara zafi kan buƙatar banbance...

  7. Batutuwan da bikin 'Ranar Hausa ta Duniya' zai mayar da hankali kai a bana

    Shirin Ala'adunmu na gado a wannan mako ya mayar da hankali ne kan 'Ranar Hausa ta Duniya' 'lokaci na musamman da ake amfani da shi wajen tunatar da muhimmancin harshen Hausa da kuma Al’adun Hausawa. Ku danna alamar sautin da ke sama domin sauraron cikakken shirin tare da Abdoullaye Issa...........

  8. Halin da ake ciki game da al'adar 'Yan Kama da ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa

    Shirin "Al’adunmu na gado, ya mayar da hankali kan fadi-tashin da ake yi don adana tsohuwar al'adar mawaƙan 'Yan Kama a ƙasar Hausa. Waƙoƙin 'Yan Kama salon fasaha ne na musamman da mawaƙan ke amfani da shi domin nishaɗantarwa, inda suke sauya shahararrun waƙoƙi su koma na maganar abinci ko cika...

  9. Wane tasiri Chamfi ke da shi wajen gyarawa ko kuma ruguza aure musamman a zamanin baya

    Shirin Al'adunmu na gado na wannan mako zai mayar da hankali ne kan yadda Chamfe-Chamfe ke shafar lamuran auratayya musamman a zamanin baya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shrin tare da Abdullahi Isa

  10. Muhimmancin zurfafa bincike a dukkan fannoni gabanin aure

    Shirin 'Al'adunmu Na Gado zai yi duba ne kan muhimmancin zurfafa bincike gabanin aure. Al’adun al’ummar Hausawa da ma mafi yawan al’ummomin da ke zaune a yankin arewacin Nigeria, sun sahale wa iyaye, gudanar da bincike kan yaron da ya nuna kai yana son ‘yarsu da aure, kamar yadda shima bangaren...

  11. Makomar makarantun gwaji na harsunan gida a Jamhuriyar Nijar.

    Shirin wannan makon zai duba makomar makarantun gwaji na harsuna gida da suka haɗa harshen Hausa. A waɗannan makarantu, za a riƙa koyarwa da harsunan gida. Za a koya wa yara sana'o'i irin na gargajiya, a kuma koya musu adabin harsshe da sauransu.

  12. Yadda Hausawa ke cin kasuwar abincin gargajiya a Saudiyya

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoullaye Issa a wannan mako ya yi duba kan yadda Hausawa ke ɗabbaƙa al'adunsu ta hanyar hada-hadar abincin gargajiya a ƙasa mai tsarki ko kuma Saudi Arabiya. Kamar yadda ya ke sanannen abu, Hausawa kan rungumi mabanbantan sabbin al'adu amma yana matuƙar wahala a...

  13. Yadda kiɗan Gurmi ke neman ɓacewa a ƙasar Hausa

    Shirinmu na yau ya leƙa sassan arewacin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, tare da duba yadda wani fitaccen kiɗan gargajiya, wato kiɗan Gurmi, ke fuskantar barazanar bacewa a fadin ƙasar Hausa. Shin me ke janyo haka, kuma wane canji fasahar zamani ta kawo? Gurmi, kayan kiɗa ne da aka sani tun kaka da...

  14. Yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da gagarumin taron sada zumunci

    Shirin Al'adun mu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda Hausawa mazauna Jamus suka gudanar da wani gagarumin taro. Ku danna alamar Saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa.

  15. Gombe: Fulani sun yi taro kan warware matsalolin da ke ɓata musu suna

    Shirin Al'adunmu na Gado a wannan mako, yayi tattaki ne zuwa garin Gombe, inda Al'ummar Fulani suka gudanar da wani taro na farfaɗo da Al'adunsu na Gargajiya, da kuma tattaunawa a kan hanyoyin da za a bi wajen maido da Tarbiyya, gami da zamantakewa kyakkyawa a tsakanin Fulanin da kuma sauran Ƙabilu.

  16. Yadda al'ummar wani gari suka riƙe Al'adar da suke kira da "Sai kowa ya zo"

    Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako tare da Abdoulaye Issa ya yi duba kan wata Al'ada da ake kira "sai kowa ya zo" a tsakanin al'ummar wani gari da ke Yankin Arewacin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron karin bayani.......

  17. Tasirin karance-karance Littattafan Hausa wajen ɗabbaƙa al'adun Hausawa

    Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan tasirin karance-karancen Littattafan Hausa a zamantakewar Al'ummar yankin. Irin waɗannan Littafai kuwa sun ƙunshi Magana Jari da jiki Magayi baya da Uwar Gulma da Shehu Umar kana Ruwan Bagaja, waɗanda...

  18. Rawar da mayaƙa suka taka zamanin da a Masarautun ƙasar Hausa

    Shirin Al’adun mu na Gado a wannan makon ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda ya duba batun da ya shafi mazajen dauri, musaman mayaƙan gargajiya a wannan zamani, jaruman da ke ƙarƙashin inuwar sarakunan gargajiya. Duk inda akwai masarautun gargajiya an san su da tarin mayaƙa da ke yin tsarin daka a...

  19. Yadda kiɗan shantu ke ƙoƙarin ɓacewa duk da shaharar da ya yi a shekarun baya

    Shirin Al'adun mu na gado na wnnann mako ya waiwayi kiɗan Shantu ne da ya shahara tsakanin Mata a shekarun baya, wanda bayan tasirin da ya yi a waccan lokaci a fagen nishaɗantarwa, kiɗan na Shantu ke neman ɓacewa a yanzu. A shekarun baya dai wannan kiɗa na Shantu ya shahara ne tsakanin mata a...

  20. Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin (2)

    Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya ɗora ne a kan yadda aka gudanar da bukukuwan addinin gargajiya na Vodun a Jamhuriyyar Benin, bikin addinin gargajiya da ke da muhimmanci a ƙasar.

  21. Yadda bikin addinin gargajiya na Vodun ke gudana a Jamhuriyar Benin

    Shirin Al'adunmu na Gado tare da Abdoulaye Issa a wannan makon, ya yi tattaki ne zuwa Jamhuriyar Benin, inda ya halarci bukukuwan addinin gargajiya na Vodun, bikin da ke da muhimmanci matuƙa a ƙasar. Tun a bara ne aka ƙara wa'adin ranakun gudanar da wannan biki wanda ke samun mahalarta daga sassa...

  22. Hausawan Turai na fuskantar barazanar ɓacewar harshe da al'adunsu

    Shirin "Al'adunmu na gado" a wannan makon tare da Nura Ado Suleiman ya leƙa ne Masarautar Hausawa da ke nahiyar Turai, inda a makon Masarautar ta karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Daura Dakta Umar Faruk Umar da ya yi tattaki daga Tarayyar Najeriya, domin halartar bikin karrama Sarkin Hausawan na...

  23. Yadda aka gudanar da bikin nuna al'adu na masarautar Jiwa a Abuja

    Shirin Al'adun gargajiya na wanan makon tare da Abdoulaye Issa ya yi duba game da yadda aka gudanar da bikin al'adu na masarautar Jiwa a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya. Shiga alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.......

  24. Yadda aka gudanar da bikin naɗin sarautar sarkin Komadugu a Maraɗi

    Shirin na yau ya yada zango jihar Diffa dake Jamhuriyar Nijar,yankin da aka gudanar da bikin nadin sabon sarkin Komadugu, wanda ya samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar. Diffa dai kamar dai yadda masana tarihi suka tabbatar, ana na nufin Diwa a harshen Kanuri kenan. Kalmar ta samo asali ne...

  25. Yadda sana'ar sassaƙar Turmi ke fuskantar koma baya sabida ci gaban zamani

    Shirin "Al'adun mu na Gado" na wannan makon ya yi duba ne akan sana'ar nan ta sassaƙar Turmin, wadda ke a matsayin sana'ar al'adun gargajiya, ko da yake a yanzu samar da na'urori da ke amfanin da Turmin keyi ya mayar da sana'ar baya matuka gaya. A baya duk macen da za'a kai gidan miji, akan…

    more
  26. Yadda ƴan siyasa ke katsalandan a harkokin masarautu a Najeriya

    Shirin al'adun mu na gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan siyasa ke katsalandan a masarautun gargajiya a Najeriya. Danna alamar sauarre domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Isa

  27. Bikin Kalankuwar farfaɗo da al'adun Hausawa a jihar Kano ta Najeriya

    Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali ne kan Kalankuwar farfaɗo da al'adunmu Hausawa a jihar Kano ta arewacin Najeriya, a wani yanayi da al'umma ke fuskantar matsalar gushewar tarin al'adu a mataki daban-daban. Yayin wannan bikin Kalankuwa dai an duba...

  28. Yadda al'adar ''Ƴar zaman Ɗaki'' ta zama tarihi tsakanin hausawa

    Shirin Al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda sananniyar al'adar nan ta zaman ɗaki ke ƙoƙarin shuɗewa tsakanin al'ummar Hausawa. Shekaru aru-aru, da zarar an yi auren budurwa a ƙasar Hausa akan haɗata da ƙaramar yarinya da za ta yi mata zaman ɗaki,...

  29. Yadda aka gudanar da bikin makiyaya na Cure Salee a Jamhuriyar Nijar

    Shirin a wannan mako ya yi tattaki ne, zuwa ƙauyen Ingal da ke Yankin Agadez a jamhuriyyar Nijar, domin waiwayar gagarumin bikin makiyaya da ƙabilu daban-daban da ake yi wa laƙabi da 'Cure Salee' wanda aka saba yi duk shekara. Bikin makiyayan na Cure Salee ya gudana ne a tsakanin ranakun 4 zuwa 6...

  30. Yadda sana'ar kaɗi ke gab da gushewa tsakanin al'ummar Hausawa

    Shirin al'adunmu na gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya mayar da hankali ne kan gushewar sana'ar kaɗi a ƙasar Hausa duk da kasancewarta guda cikin sana'o'in Hausawan suka gada kaka da kakanni. Galibi sana'o'in Hausawa na tafiya ne da tsarin rayuwa da zamantakewar jama'a, cikin wannan...

  31. Banbanci tsakanin maita da tsafi a mahangar al'adu da addini

    Shirin Al'adunmu na Gado tare da Nura Ado Suleiman a wannan mako, ya mayar da hankali kan manufar Maita da kambun baka a mahangar al'adu da kuma addini, a wani yanayi da ake yiwa wannan abubuwa biyu mabanbantan kallo. Duk da cewa wasu na yiwa waɗannan abubuwa biyu kallon abu guda, amma a wasu na...

  32. Yadda aka bar baya da ƙura a girmamawar da ka yiwa Rarara da digirin Dakta

    Shirin Al’adunmu na Gargajiya tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon ya sake waiwayar fagen Waƙa guda daga cikin fannoni masu tasiri a Adabin Harshen Hausa la’akari da gudunmawar waƙoƙin da kuma mawaƙan da ke rera su wajen bunƙasa harshen. Tun cikin makon jiya masana da sauran jama’ar gari ke...

  33. Sannu a hankali sana'ar ƙira na shuɗewa a jihar Agadez ta Jamhuriyar Nijar

    Shirin Al'adunmu na Gado na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda sannu a hankali sana'ar kira ke shudwa musamman ta ƴan Kabilar Abzinawa da ke jihar Agadez a jamhuriyar Nijar. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abdullahi Issa.

  34. Bikin cika shekaru 10 da fara Ranar Hausa ta Duniya - kashi na biyu

    Shirin Al’adunmu na Gado a wannan makon ya ɗora ne akan Bikin ranar Hausa ta Duniya, bikin da yake mayar da hankali wajen bunƙasawa da faɗaɗa harshe da kuma al’adun Hausawa a fadin Duniya. A watan Agustan shekarar 2015 aka fara gudanar da wannan biki na ranar Hausa ta Duniya a Najeriya da sauran...

Topics in this show

Click any topic to search every transcript on PodParley for moments someone mentioned it.

About this show

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

Hosted by

RFI Hausa

Produced by France Médias Monde

Categories

Frequently asked questions

How many episodes does Al'adun Gargajiya have?

Al'adun Gargajiya has 34 episodes on PodParley. The most recent episode was published on October 27, 2026.

What is Al'adun Gargajiya about?

Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

How often does Al'adun Gargajiya release new episodes?

Al'adun Gargajiya publishes weekly, based on its 34 episodes since December 2025.

Who hosts Al'adun Gargajiya?

Al'adun Gargajiya is created and hosted by RFI Hausa.
Link copied