Skip to content
Kasuwanci podcast artwork

PODCAST · business

Kasuwanci

by RFI Hausa

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

Publisher-supplied feed metadata · PodParley refreshed Oct 14, 2026 · Source feed

Episodes

  1. Borno na son farfado da tattalin arzikin waɗanda ricikin Boko Haram ya ɗaiɗaita

    Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin jihar Borno da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al'ummar da rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita. Bayan kwashe...

  2. Rahoton CBN ya ce ƙarfin sayayyar ƴan Najeriya ya ƙaru a watan Satumba

    Yau shirin zai mayar da hankali kan sabon rahoton Babban Bankin Nigeria, wanda ya fito da sabbin alkaluman ci gaban da aka samu a fannin damar iya sayen kayayyaki a kasuwanni a tsakanin al’ummar kasar da ya karu da maki 53 a watan Satumba daga maki 52.7 daga watan Agustan da ya gabata. Madallah!...

  3. Dalilin da ya sanya aka fara haramta sana'ar jari bola a wasu sassan Najeriya

    Sana’ar tattara wa da sayar da tsofaffin ƙarafa da sauran tarkace wadda aka fi sani da ‘Bola Jari’ na daga cikin sana’o’i da dubban mutane masamman matasa ke dogaro da su a Najeriya. Amma a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan, sana’ar ta fuskanci babban ƙalubale, musamman saboda zargin cewa wasu...

  4. Matatar matatar Ɗangote ta ƙaddamar da sayar da hannayen jarinta a hukumance

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan ƙaddamar da shiga matatar Ɗangote kasuwannin hannayen jarin Najeriya, a wani biki da aka gudanar a babban shelkwatan kasuwannin hannayen jarin Najeriya da ke Marina a birnin Legas, inda shugaban rukunin kamfanonin Dangote…

    more
  5. Tasirin da saida hannun jarin matatar man Dangote ke da shi ga al'umma

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan lokacin, ya maida hankali ne kan yadda matatar Dangote ta shirya buɗe ƙofifinta ga al’umma domin su mallaki wani kaso a matatar mafi girma a Afirka, bayan da a karon farko ta sanar da shiga kasuwar hannayen jari. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken...

  6. Sharhi kan kalaman Alhaji Atiku na maido da tallafin mai a Najeriya

    Shirin ‘kasuwa akai miki dole’ a wannan mako tattauna ne kan wasu batutuwa da suka taso masu nasaba da siyasa da tattalin arziƙi a Najeriya, Inda muhawara ta kaure kan batun tallafin man fetur, bayan da ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar adawa ta ADC Alhaji Atiku Abubakar ya yi alƙawarini...

  7. Ghana ta zama ƙasa ta 6 a cikin jerin ƙasashen da ke samar da zinari a duniya

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya maida hankali ne kan yadda Ghana ta zama ta shida a cikin manyan ƙasashe da suka fi samar da zinare a duniya, bayan zarce Amurka a alƙaluman yawan zinare da ƙasar ta yammacin Afirka ta hako a shekarar 2025 da ta gaba. To, amma menene tasirin...

  8. Me cigaban kasuwar hannayen jarin Najeriya ke nufi ga talakan ƙasar kashi na 2

    Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya dora kan shirin makon da ya gabata, wanda ya mayar da hankali kan ci gaba da kasuwar hannayen jarin Najeriya ta samu, wajen zama ta ɗaya a duniya, kamar yadda mujallar Bloomberg ta sanar a ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta...

  9. Cigaban kasuwar hannayen jari na nufin rayuwa ta fara inganta ga talakan Najeriya?

    A ƙarshen watan Yulin wannan shekara ta 2026, mujalar Bloomberg da ke bibiyar harkokin tattalin arzikin ƙasashen duniya, ta bayyana kasuwar hannayen jarin Najeriya a matsayin ta ɗaya a duniya a fannin dala, wajen yi wa ta Koriya ta Kudu fintinƙau. Masana tattalin arziki sun alakanta wannan...

  10. Ghana ta yiwa ƙasashen Afrika fintinkau a fannin ci gaban hada-hadar kuɗaɗe ta wayar hannu

    Shirin na wannan mako ya duba yadda Ƙasar Ghana ta zama jagaba a fannin hada_hadar kuɗi ta wayar hannu a Afirka, inda a wannan shekara kaɗai kamfanonin sadarwar wayar tafi da gidanka suka yi hada-hadar sama da Cidi biliyan 40. Ku danna lamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

  11. Illar cushen kusan naira tiriliyan 1 a kasafin kuɗin Najeriya ga tattalin arziƙi

    Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako, ya mayar da hankali ne kan yadda aka gano cushen kusan Naira triliyan ɗaya cikin kasafin kuɗin Najeriya na wannan shekarar ta 2026, domin sayen motocin alfarma da kuma ayyukan tallafa wa jama'a. Wannan na ƙunshe ne cikin wani rahoton…

    more
  12. Matakin matatar Ɗangote ya fusata ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya

    Shirin a wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi dubi ne kan matakin da ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu a Najeriya ta sanar na dakatar da sayen mai daga matatar Dangote, sakamakon matakin da matatar ta ɗauka na fara sayar musu da man da take tacewa da dala maimakon Naira. Shiga alamar...

  13. Rashin rassan bankuna ya tilastawa al'ummar karkara rungumar POS a Najeriya

    Shirin kasuwa akai miki dole dake bibiyar harkokin kasuwanci da tattalin arziki na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ci gabar fasahar zamani da aka samu a fannonin haɗar-haɗur ƙudi a Najeriya, ke shafar al’ummomi a yankunan ƙarƙara.

  14. Ana samun ƙaruwar cin bashin kuɗin kiran waya tsakanin jama'ar Najeriya

    Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda ƴan Najeriya suka rungumi ɗaukar bashin kiran waya, wanda wani rahoto ya ce, a bara kaɗai anci bashin kiran waya da ƙudinsu ya kai Naira Tiriliyan 4 da biliyan 61. Wasu bayanai da cibiyar fintech...

  15. Yadda tattalin arzikin Ghana ke haɓɓaka sannu a hankali

    Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane yadda tattalin arzikin ƙasar Ghana ke ci gaba da ɓunƙasa sannu a hankali. Ku danna alamar sauraro domin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

  16. Koken ƴan Najeriya kan yadda bankuna ke zare musu kuɗi daga asusun ajiyarsu

    Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan yadda ƴan Najeriya, ke nuna fushinsu dangane da zargin cire musu kuɗi ba bisa ka’ida ba daga asusun bankunansu. Miliyoyin 'yan Najeriya da yanzu haka ke fuskantar hauhawan farashin kayayyaki da kuɗin sufuri, da kuma...

  17. Yadda ƴan kasuwa a Najeriya suka jingine harakokinsu saboda tsadar sufuri

    Shirin Kasuwa akai miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.......

  18. Yadda tsadar sufuri ya tilastawa 'yan kasuwa jingine sana'o'insu a Najeriya

    A yau shirin ya mayar da hankali ne kan yadda a Najeriya, 'Yan kasuwa da dama suka fara jingine harkokinsu saboda yadda tsadar sufuri ke cinye ribar da suke samu, wasu lokuta har da jarinsu . Sannu a hankali, irin hada-hadar da aka saba gani tsakanin mafi yawan kasuwannin Nigeria na neman zama…

    more
  19. Damarmaki da kuma ƙalubalen da manoman Albasa a arewacin Kamaru ke fuskanta

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon, ya duba ƙalubale da kuma damammaki a ɓangaren noman albasa a arewacin Kamaru. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

  20. Matakan da bankin CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗi a Najeriya

    Shirin Kasuwa akai miki doke na wannan mako ya yi duba ne kan matakan da babban bankin Najeriya CBN ke ɗauka na sake fasalin tsarin harkokin kuɗaɗe, domin rage hauhawan farashin kayayyaki a kasuwanni da kuma daga darajar kuɗin ƙasar wato Naira, ta hanyar rage kuɗaɗe da ke yawo a hannun jama’a....

  21. Yadda matsalolin tsaro ke kassara kasuwanci a arewacin Najeriya

    Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin fargabar da 'yan kasuwar arewacin Najeriya da ke fatauncin kayayyaki zuwa wasu sassan jihohi ke ciki, sakamakon ayyukan bata gari da ke tare hanya wanda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuka. Abune da aka saba gani, ‘yan kasuwar dake hada Hada...

  22. Yadda matasa ke fatan cin gajiyar yarjejeniyar tattalin arziki tsakanin Nijar da Algeria

    Matasa a Agadez da ke arewacin Jamhuriyar Nijar na cike da fatan cin moriyar sabuwar dangatakar da aka kyautata tsakanin kasar da makwabciyarsu Aljeriya. Ku danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

  23. Koma bayan da kasuwancin duniya ya fuskanta sakamakon rikicin Gabas Ta Tsakiya

    Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" tare da Ahmed Abba a wannan mako ya ɗora ne kan inda ya tsaya a makon jiya, game da gagarumin koma baya a fannin kasuwanci da tattalin arziki da duniya ke fuskanta masamman a bangaren makamashi, sakamakon yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran…

    more
  24. Yadda yaƙin Iran ya haifar da koma baya ga tattalin arzikin Duniya

    A yau shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne a kan yadda Yaƙin da kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran, da hare-haren mayar da martini na jamhuriyar musuluncin kan yahudun Isra’ila da muradun Amurka a kasashen labarawa suka janyo...

  25. Yadda aka gudanar da taron tattalin arzikin a Akwa Ibom

    Shirin Kasuwa A kai Miki Dole na wanan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan taron taron tattalin arziki da ya gudana a farkon watan Fabarairun da ya gabata a jihar Akwa Ibom da ke kudancin Najeriya. Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....

  26. Najeriya da China sun yi bukin cika shekaru 55 da hulɗar diflomasiyya

    Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan tasirin tattalin arziki dangane da alaƙar China da Najeriya da a makon jiya aka yi bikin cika shekaru 55 da faro hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu. Najeriya da China sun sake jaddada karfafa...

  27. Yadda buɗe iyakokin Najeriya da Nijar zai taimaka wajen haɓaka kasuwanci

    Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan wani sabon yunkuri na kara inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar inda hukumar kwastom a jamhuriyar Nijar tayi tattaki zuwa Najeriya don tattaunawa hanyoyin da za’a bi don saukaka hada-hadar kayayyaki...

  28. Yadda gwamnatin jihar Yobe ta duƙufa wajan gina kasuwannin zamani

    Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan gina kasuwanni na zamani da Gwamnatin Jihar Yobe ta sake ginawa a wasu sassan jihar domin karfafa harkokin kasuwanci da suka fuskanci koma baya, saboda matsaloli na Boko Haram. Shiga alamar sauti domin…

    more
  29. Yadda aka ƙulla yarjejeniyar kasuwanci mafi girma a duniya tsakanin India da EU

    Yau shirin ya mayar da hankali ne dangane gagarumar yarjejeniyar cinikayya mafi girma da ba’a taba ganin irinta ba, da aka cimma tsakanin ƙungiyar Tarayyar Turain ƙasar India. Yarjejeniyar da aka cimma yayin ziyarar da shugabannin Turai suka kai New Delhi na ƙasar India, za ta bada damar…

    more
  30. Mahangar masana kan kiran IMF da bankin Duniya ga Najeriya don sauƙaƙa tsadar rayuwa

    Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole"na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan sabbin kiraye-kirayen da Bankin Duniya da kuma Asusun bada Lamuni na Duniya (IMF) suka yi ga gwamnatin Najeriya wajen ganin ta ɗauki matakab da suka kamata don ƙara rage hauhawar farashin kayayyaki domin…

    more
  31. Yadda Najeriya ta yi iƙirarin rarar tiriliyan 12 a watanni 6 farkon 2025

    Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali kan ikirarin gwamnatn Najeriya na samun rarar kuɗi da ya kai tiriliyan 12 kuma kashi 21 daga ciki ta same su ne daga bangarorin da ba na man fetur ba a cikinn watanni 6 na farkon shekarar 2025. Ku latsa alamar…

    more
  32. Tasirin kama shugaba Maduro na Venezuela ga tattalin arzikin duniya

    Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya tattauna da masana da sauran masu ruwa da tsaki kan harkokin man fetir dangane da tasirin kama shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro da Amurka ta yi zai yi ga tattalin arzikin duniya.

  33. Hangen masana tattalin arziƙi kan sabon harajin gwamnatin Najeriya

    Shirin "Duniya Akai Miki Dole" tare da Faruk Muhammad Yabo a wannan mako ya yi duba ne kan sabbin harajin da gwamnatin Najeriya ke shirin karɓa a hannun jama'ar ƙasar, a wani yanayi da ƙasar ke fatan tattara wani ɓangare na kuɗaɗen tafiyar da harkokinta. Shirin a wannan mako ci gaba ne na makon…

    more
  34. Abubuwan da sabon tsarin harajin Najeriya ya ƙunsa

    A wannan mako shirin zai tattauna ne kan sabuwar dokar harajin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya wa hannu, wadda kamar yadda na ambata ba da jimawa, za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan gobe na shekara mai zuwa. Tun a watan Yunin da ya gabata shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar...

  35. Al'ummar Nijar sun rungumi tsarin hada hadar kuɗi ta manhajar waya

    Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako ya leka Jamhuriyar Nijar ne, inda a shekarun baya bayan nan, hada hadar kuɗi ke neman yin ƙaura daga bankuna zuwa manhajojin wayar salula da ake kira da Mobile Money a Turance, da ake amfani da tsarin wajen aikewa da kuɗi ko karɓarsu a ciki da wajen...

  36. Yan Najeriya na yawaba Hasetins kan kafa kamfanin ma'adanai mafi girma a Afirka

    Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali ne kan gina katafaren kamfanin tono da kuma sarrafa ƙarafu da duwatsu masu daraja da wani matashi ya ƙaddamar a jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya, irinsa mafi girma a Afirka, wanda zai laƙume dalar Amurka...

  37. Shin yaya harajin da bankuna ke cirewa ƴan Najeriya a asusunsu ke shafar tattalin arziki

    Shirin Kasuwa a kai Miki Dole na wannan mako ya mayar da hankali ne kan binciken da majalisar wakilan Najeriya ta ƙaddamar bayan ƙorafin ƴan ƙasar game da yawan haraji da bankuna ke cirewa a asusun su na ajiya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Ahmad Abba.

Type above to search every episode's transcript for a word or phrase. Matches are scoped to this podcast.

Searching…

We're indexing this podcast's transcripts for the first time — this can take a minute or two. We'll show results as soon as they're ready.

No matches for "" in this podcast's transcripts.

Showing of matches

TOPICS IN THIS SHOW

Click any topic to search every transcript on PodParley for moments someone mentioned it.

Loading reviews...

ABOUT THIS SHOW

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

HOSTED BY

RFI Hausa

Produced by France Médias Monde

CATEGORIES

Frequently Asked Questions

How many episodes does Kasuwanci have?

Kasuwanci currently has 37 episodes available on PodParley. New episodes are automatically indexed when they're published to the podcast feed.

What is Kasuwanci about?

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

How often does Kasuwanci release new episodes?

Kasuwanci has 37 episodes. Check the episode list to see recent publication dates and frequency.

Where can I listen to Kasuwanci?

You can listen to Kasuwanci on PodParley by clicking any episode. We provide an embedded audio player for direct listening, and you can also subscribe via your preferred podcast app using the RSS feed.

Who hosts Kasuwanci?

Kasuwanci is created and hosted by RFI Hausa.
URL copied to clipboard!