Kanun Labaran Hausa na Asabar, Ranar Salla 2026-03-21 episode artwork

EPISODE · Mar 21, 2026 · 3 MIN

Kanun Labaran Hausa na Asabar, Ranar Salla 2026-03-21

from Hausa Newsletter · host Hausa Radio News Headlines

2026-03-21 Saturday-AsabarBBC Hausa SafeMai gabatarwa: Muhammad Annur Muhammad* Shugaba Trump ya ce Amurka na tunanin dakatar da yaƙin da take yi a Iran. Amma kuma kafofin yaɗa labarai na cewa ma’aikatar tsaron Amurka na duba yiwuwar tura sojin ƙasa cikin Iran ɗin.* Kasuwannin hannun jari a Amurka sun ƙara... wato sun ƙare wannan makon da ke zaman na uku (3rd week) da fara yaƙin taron dangi na Amurka da Isra’ila da Iran, da darajarsu ta yi ƙasa sosai.* A Najeriya ana ci gaba da cece-kuce kan wata yarjejeniya da ƙasar ta ƙulla da Birtaniya inda za ta karɓo wasu fursunoni daga ƙasar ta turai.* Gidajen da muke da su na kaso a faɗin Najeriya baki ɗaya. Babu wani guda ɗaya wanda za a ce yana da sufayan (spare) ɗaki ko ɗakuna da za a iya sa waɗannan mutane. To ina ake tunanin sa su?* Har wa yau a Najeriyar, rikicin jam’iyyar hamayya ta ADC ya ɗauki wani sabon salo inda wani ɓangare ya nemi Amurka ta ɗauki mataki a kan ɗaya ɓangaren da yake ja-in-ja da shi.* Muna so Amerika ta ayyana waɗannan mutane a matsayin maƙiya dimokuraɗiya a ƙasanmu Najeriya. Ta saka musu takunkumi da kowane motsi da za su yi. Saboda suna da rakot (record) na wannan kawo irin waɗannan fitintunun a kowace jam’iya suka shiga.* Muna kuma tafe da filin gani. Muna hanya da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido.DW HausaCikakken shirin | Mai gabatarwa: DW Hausa’s Binta Aliyu Zurmi da Khadija Ahmad Rufa’i* Za mu leƙa a wasu jihohin Najeriya domin jin yadda ake cigaba da gudanar da shagulgulan sallah.* Yadda aka gudanar da liyafar cin abincin Sallah a sashen Hausa na DW [YouTube]* Tuwon Sallah: Ina zamani ya kai shi? https://www.bbc.com/hausa/articles/cn03n6e479vo* A daidai lokacin da rikici ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya, Shugaban Amurka Donald Trump na duba yiwuwar sassauta takunkumin man fetur da aka ƙaƙaba wa ƙasar Iran.* Cocin Orthodox ta Rasha na ƙara samun tagomashi a nahiyar Afirka a ƴan shekarun baya-bayan nan.* Shugaban ƙasar Venezuela ta yi garan bawul mafi girma a rundunar tsaron ƙasar.* Rasha ta sake lugudan wuta a cibiyoyin makamashin Ukraine.* Mujtaba Khamenei ya ce Tehran ta ci galaba a kan maƙiyansu a yaƙin da suke gwabzawa da Amurka da Isra’ila. This is a public episode. If you would like to discuss this with other subscribers or get access to bonus episodes, visit hausa.substack.com

Episode metadata supplied by the publisher feed · Published Mar 21, 2026

Embed this episode

NOW PLAYING

Kanun Labaran Hausa na Asabar, Ranar Salla 2026-03-21

0:00 3:00

No transcript for this episode yet

We transcribe on demand. Request one and we'll notify you when it's ready — usually under 10 minutes.

No similar episodes found.

No similar podcasts found.

Frequently Asked Questions

How long is this episode of Hausa Newsletter?

This episode is 3 minutes long.

When was this Hausa Newsletter episode published?

This episode was published on March 21, 2026.

Can I download this Hausa Newsletter episode?

Yes. Use the download control on the episode player to save the publisher-provided media file.
URL copied to clipboard!