EPISODE · Feb 26, 2026 · 18 MIN
Me Nadin Sabon Sufeton 'Yansanda Ke Nufi Ga Tsaron Cikin Gida Najeriya?
from Najeriya a Yau · host Idris Daiyab Bature
Send us Fan MailShugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), matakin da ya sake jawo hankalin al’umma kan makomar tsaro da gyaran harkokin rundunar ‘yan sandan ƙasar nan. Naɗin sabon jagoran rundunar ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙalubale daban-daban na tsaro, ciki har da satar mutane, ta’addanci, da rikice-rikicen cikin gida a wasu sassan ƙasa.Sabon Sufeton ana sa ran zai ɗora kan nasarorin da aka samu a baya tare da kawo sababbin tsare-tsare da dabarun da za su ƙarfafa yaƙi da laifuka, inganta hulɗa tsakanin ‘yan sanda da al’umma, da kuma farfaɗo da martabar rundunar. Ko ta yaya wannan naɗin sabon shugaban ‘yansandan zai amfani tsaron cikin gida Najeriya?Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Embed this episode
Ready to play
Me Nadin Sabon Sufeton 'Yansanda Ke Nufi Ga Tsaron Cikin Gida Najeriya?
No transcript for this episode yet
Similar Episodes
No similar episodes found.
Similar Podcasts
No similar podcasts found.