EPISODE · Feb 24, 2026 · 20 MIN
Shin Da Gaske An Fara Samun Ɓaraka Tsakanin Atiku Abubakar Da Peter Obi A Tafiyar ADC?
from Najeriya a Yau · host Idris Daiyab Bature
Send us Fan MailRahotanni daga sassa daban-daban na siyasar Najeriya na nuna cewa ana fara samun ɓaraka a tsakanin manyan jiga-jigan haɗakar tafiyar ADC, musamman tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi.Ko da yake har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma da ke tabbatar da wannan saɓani, majiyoyi na nuni da cewa sabanin ra’ayi kan jagoranci, tsarin tafiya, da kuma makomar zaɓen 2027 na iya zama tushen wannan rikici.Wasu masu sharhi na ganin cewa irin wannan saɓani abu ne da kan taso a duk wata haɗaka ta siyasa, musamman idan manyan ‘yan takara masu farin jini suna ƙoƙarin haɗa kai domin cimma buri ɗaya. Sai dai tambayar ita ce: shin wannan ɓaraka za ta iya raunana haɗakar kafin ta kai ga gaci, ko kuwa za a samu sulhu a tsakaninsu?A yau, shirin Najeriya A Yau zai yi duba ne kan gaskiyar lamarin, me ke haddasa wannan jita-jita, da kuma irin tasirin da hakan zai iya yi ga makomar siyasar Najeriya.
Embed this episode
What this episode covers
Send us Fan Mail Rahotanni daga sassa daban-daban na siyasar Najeriya na nuna cewa ana fara samun ɓaraka a tsakanin manyan jiga-jigan haɗakar tafiyar ADC, musamman tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi. Ko da yake har yanzu babu wata sanarwa ta hukuma da ke tabbatar da wannan saɓani, majiyoyi na nuni da cewa sabanin ra’ayi kan jagoranci, tsarin tafiya, da kuma makomar zaɓen 2027 na iya zama tushe...
NOW PLAYING
Shin Da Gaske An Fara Samun Ɓaraka Tsakanin Atiku Abubakar Da Peter Obi A Tafiyar ADC?
No transcript for this episode yet
Similar Episodes
No similar episodes found.
Similar Podcasts
No similar podcasts found.